Kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky, ya sheda a ran 21 ga wata cewa, an tsawaita wa'adin aikin wakilin musamman na MDD da AL mai kula da rikicin kasar Sham Lakhdar Brahimi zuwa karshen wannan shekara.
Haka zalika an kara wa'adin aikin mataimakin wakilin musamman Nasser al-Kidwa, da jami'in ofishin wakilan musamman mai kula da rikicin kasar dake birnin Damascus Mukhtar Ramani.
Idan dai ba a manta ba, an nada tsohon ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Lakhdar Brahimi ne, a matsayin wakilin musamman a ran 17 ga watan Agusta na shekarar 2012, aka kuma rantsar da shi a ran 1 ga watan Satumba, domin maye gurbin Kofi Annan wanda ya gama aikin sa ran 31 ga watan Agusta, bayan kammala wa'adin sa na farko.
Wa'adin farko na Lakhdar Brahimi dai na tsawon watanni shida,zai kare ne a Jumma'ar nan 22 ga wata.
Bayan Lakhdar Brahimi ya hau kan kujera ya yi iyakacin kokarin shiga tsakani a wasu kasashe, kuma ya taba kai ziyara sau da dama a kasar Sham da dai sauran kasashen dake yankin gabas ta tsakiya, har ma ya gana da shugabanni a wannan yanki ciki hadda Bashar Al-Assad shugaban kasar Sham. A karshen watan Disamba na shekarar bara, Lakhdar Brahimi ya kawo karshen ziyararsa a kasar Sham karo na uku tare kuma da gabatar da sabuwar shawarar warware rikicin kasar Sham, ciki hadda kafa wata gwamnatin wucin gadi mai karfi a kasar. (Amina)