Rahoton ya nuna cewa, bangarorin biyu dukkansu sun kashe fararen hula da kuma masu shiga rikici yayin da ake cikin yanayin kwanciyar hankali a kasar.
Ya kuma kara da cewa, bangarorin biyu suna da hannu cikin aikace-aikacen bata hakkin yara da suka hada da kisan yara, da kuma yi musu zalunci.
Shugaban kwamitin bincike Paulo Pineiro ya jadadda cewa, kamata ya yi bangarorin biyu dake rikici a kasar Syria su tsayar da dukkan aikace-aikacen tashin hankali tsakaninsu ta hanyar siyasa, kuma a yi wa masu laifin yaki hukunci.
A wannan rana, jakadan kasar Rasha da ke kasar Lebanon Alexander Zasypkin ya bayyana a birnin Beirut cewa, kada a raba kai yayin warware matsalar Syria, sabo da kasar Rasha na ganin cewa, hanyar da ta fi dacewa wajen warware matsalar Syria ita ce a yi shawarwari tsakanin bangarorin daban daban na kasar Syira, kuma wannan hanya za ta iya biyan bukatun jama'ar kasar, na ci gaban kasa cikin yanayin zaman lafiya. (Maryam)