Kafar ta bayyanawa jaridar cewa sun gabatar da wani rahoto ga shugaba Benjamin Netanyahu dangane da samar da wata kariya a bayan ko kuma kafin rushewar gwamnatin shugaba Assad.
Rahoton ya ci gaba da cewa wannan tanadi ko kuma mataki na tsaro ya kunshi gina shingen tsaro mai tsawon kilomita 16 a yankin tuddan Golan, wato yankin da Israila ta kwace a yakin 1967.
A matakin farko dai, zaa girke sojoji da tankokin yaki na soja a cikin yankin kasar Syria.
Yayin da ake ci gaba da nazarin wannan mataki, sojin kasar Isra'ila ta kara kaimi kan wani aiki da ya fara a shekarar da ta wuce, wato na aikin samar da katanga ta musamman da ke aiki da fasahar zamani a kan iyakar.
A shekarar da ta wuce an gina kilomita 9 cikin kilomita 70 na tsawon katangar wacce ta kunshi karafuna masu tsayin mita shida, kuma ana sa ran cewa zaa kare wannan aiki a tsakiyar shekarar 2013.
A farkon watan Janairu, shugaba Netanyahu ya ce aikin gina katangar wanda zai lashe dalar Amurka miliyan 70, aiki ne na maimaita nasara da aka cimma na gina katangar da aka kammala kwanan nan a kan iyakar yammacin Israila da kasar Masar.