in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 53 sun mutu sakamakon fashewar bom a kasar Sham
2013-02-22 16:47:02 cri

An kai harin kunar bakin wake cikin wata mota a wurin kusa da hedkwatar jam'iyyar farfado da kasa wadda ke jan ragamar mulkin kasar a ran 21 ga wata.

Ya zuwa yanzu dai, an ce mutane a kalla 53 sun mutu, yayin da wasu fiye da 200 suka samu rauni.

Da kimanin karfe 11 na wannan rana da safe ne, wata mota da aka dasa bom a cikinta ta fashe a wata mararrabar titin al-Thawra dake unguwar Mazraa a birnin Damascus hedkwatar kasar Sham, kusa da hedkwatar jam'iyyar farfado da kasa, wani masallaci har ma da wata makaranta.

Galibin mutanen da suka mutu ko kuma suka ji rauni fararen hula ne, ciki hadda kananan yara. Gwamnatin kasar ta ce, 'yan ta'adda ne suka aikata wannan laifi, amma har yanzu ba wani mutum ko wata kunigya ta dauki alhakin aiwatar da lamarin.

Bugu da kari, a wannan rana, an samu karin fashewar boma-bomai da hare-hare a birnin Damascus, inda rokoki biyu suka fado a ginin sojin kasar Sham. Ban da haka, mutane 7 sun mutu sakamakon fashewar bom a unguwar Barzeh dake arewa maso gabashin birnin.

A ran 21 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa ta hannun kakakinsa, wadda a ciki ya kai zazzafar suka kan hare-haren fashewar boma bomai da aka samu a birnin Damascus, kuma ya tisa magana cewa, daidaituwa ta fuskar siyasa ta zama hanya daya tak da za a bi domin warware rikicin kasar Sham.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China