Bisa shirin kasar Amurka, za ta gudanar da gwajin a wani sansanin sojan sama ne da ke jihar California a wannan mako.
Kakakin majalisar gudanarwar kasar Amurka Victoria Nuland ta nuna cewa, a halin yanzu, ba a iya gane shirye-shiryen da kasar Koriya ta Arewa ke yi, don haka kasar Amurka za ta karfafa matakan tsaronta, tare da dukufa matuka, wajen kiyaye tsaron kasashen Japan, da Koriya ta Kudu da dai sauran kasashen dake yankin.
A sa'i daya kuma, kafofin watsa labarai da wasu masanan da abin ya shafa, na yin kira ga shugaba Barack Obama, da ya karfafa cudanya da hadin gwiwa tare da kasar Sin, don sassauta yanayin kota kwana, a makurdadar Koriya cikin 'yan kwanakin nan.
Bugu da kari, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, zai kai ziyarar aiki a kasashen Koriya ta Kudu, da Sin, da kuma Japan tun daga ranar 12 zuwa ta 14 ga watan Afrilu da muke ciki. (Maryam)