Labarin ya kuma nuna cewa, rundunonin kasar Koriya ta Kudu da kasar Amurka suna ganin cewa, kila kasar Koriya ta Arewa ta yi gwajin harba makami mai linzami na matsakaicin zango wanda nisan tafiyarsa zai kai kilomita dubu 3 ko dubu 4, a wani filin gwajin da ke Musudan-ri na jihar Hamgyongbukdo,don haka za su kara karfin sa ido kan yunkurin da Koriya ta Arewa ke yi.
Bugu da kari, bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya bayar ran 4 ga wata, an ce, hukumomin leken asiri na Koriya ta Kudu da na Amurka sun samu labarin cewa, kasar Koriya ta Arewa ta riga ta yi jigilar makami mai linzami na matsakaicin zango, zuwa gabar tekun gabas. (Maryam)