Wasu rahotannin baya bayan nan da suka fito daga ma'aikatar dunkule ayyukan hukuma ta kasar Koriya ta Kudu, ta bayyana cewa, makwafciyarta Koriya ta Arewa, ta katse hanyar sadarwa ta kota-kwana dake tsakinin kasashen biyu, bayan da a baya ta yi gargadin aiwatar da hakan cikin makon da ya gabata.
Ma'aikatar wadda ta bayyana hakan a ranar Litinin din nan, ta kara da cewa, layin sadarwar na gaggawa, ana amfani da shi ne a ayyukan da suka shafi yankin nan kebantacce na Panmunjom, wanda ya raba kasashen biyu, wanda kuma aka amince da haramcin jibge sojoji a cikinsa.
A wani labarin kuma kasar Koriya ta Kudu da hadin gwiwar Amurka, sun fara gudanar da wani atisayen soji tun daga Litinin din nan, har izuwa ran 21 ga wannan wata na Maris, duk kuwa da barazanar yanke yarjejeniyar tsagaita yaki ta shekarar 1950 zuwa 1953 da Koriya ta Arewan ta yi, domin nuna adawar ta da wannan atisayen soji.(Saminu)