A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana a birnin Madrid, Ban ki-moon ya ce, halin da ake ciki yanzu a zirin Koriya na ci gaba da tsananta, kuma muddin aka yi kuskure wajen yanke shawara game da halin da ake ciki a yankin, hakan na iya haddasa mummunan sakamako.
Sabo da haka, ya nuna fatan cewa Koriya ta Arewa za ta canja manufar da take bi kuma ta kai zuciya nesa. Ya ci gaba da cewa, bisa rahoto da aka samu game da harkokin tsaro da aikin jin kai da ake ciki a wurin, ana gani lamarin na iya kawo damuwa sosai.(Bako)