in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya yi shawarwari kan batun gwajin makaman nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi
2013-03-06 11:15:45 cri
A ranar 5 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya yi shawarwarin sirri kan batun gwajin makaman nukiliya karo na uku da kasar Koriya ta Arewa ta yi.

An sanar da dakatar da shawarwarin bayan fara gudanar da su na tsawon mintuna 20. Zaunanniyar wakiliyar kasar Amurka dake MDD Susan Elizabeth Rice ta bayyana wa 'yan jarida bayan shawarwarin cewa, kasarta ta gabatar da wani shirin kuduri game da gwajin makaman nukiliyar da kasar Koriya ta Arewa ta yi a ranar 12 ga watan Febrairu. Kana ta ce, takunkumin da aka sanya a cikin shirin kudurin zai taimaka wajen hana kasar Koriya ta Arewa ta ci gaba da inganta makaman nukiliya da makamai masu linzami. Kuma ta ce, za a jefa kuri'a kan shirin kudurin a cikin makon nan.

Kakakin hukumar koli ta bada umurnin sojin jama'ar kasar Koriya ta Arewa ya bayyana a ranar 5 ga wata cewa, game da takunkumin da kasar Amurka da Koriya ta Kudu suka kakabawa kasarsa da kyamar da suke nunawa, rundunar sojojin jama'ar kasarsa za ta dauki matakai uku, ciki har da kin amincewa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a makurdadar Koriya da aka daddala a shekarar 1953. Dangane da haka, kakakin fadar shugaban kasar Amurka wato White House Jay Carney ya bayyana cewa, tsokanar da kasar Koriya ta Arewa ta yi ba za ta kaita ga nasara ba, kuma za ta kawo illa gare ta da kuma zaman lafiyar yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China