logo

HAUSA

Kasar Sin ta ba da gudunmawar kayayyakin hunturu ga yaran Falasdinawa a sansanin ’yan gudun hijira

2024-11-27 10:37:07 CMG Hausa

A ranar 25 ga wata, ofishin kasar Sin da ke kasar Falasdinu ya gudanar da bikin bayar da gudummawar kayayyakin sanyi ga yaran Falasdinawa ta hannun gidauniyar Abbas ta Falasdinu a sansanonin ’yan gudun hijira guda biyu da ke birnin Tulkarem da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.

A yayin bikin bayar da gudunmawar, darektan ofishin kasar Sin da ke kasar Falasdinu Zeng Jixin, ya ce, kasar Sin tana goyon bayan maido da hakkin al’ummar Falasdinu bisa gaskiya, da tabbatar da adalci gare su, kana tana yin iyakacin kokarinta wajen ba da taimakon jin kai da na samun ci gaba ga Falasdinu. Ya kara da cewa, ofishin kasar Sin da ke Falasdinu ya hada kai da gidauniyar Abbas tsawon shekaru don ba da gudunmawar kayayyaki ga sansanonin ‘yan gudun hijira na Falasdinu. Samar da tufafin sanyi ga yara a sansanonin ’yan gudun hijira guda biyu a Tulkarem a wannan karo, wani mataki ne na zahiri na nuna soyayya da abokantaka, wanda ke fayyace tsayin dakar da kasar Sin ta yi ga al’ummar Falasdinu.

A nasa bangaren, jami’in Falasdinu a wajen bikin bayar da gudunmuwar ya bayyana cewa, jama’ar kasar sun yi matukar farin ciki da irin gudunmawar kayayyakin da kasar Sin ta ba sansanin ’yan gudun hijira a wannan karo, lamarin da ke nuna cikakken goyon bayan da kasar Sin ke bai wa al’ummar Falasdinu, Palasdinu kuma na alfahari da kara dankon zumuncin a tsakanin jama’ar kasashen biyu. (Bilkisu Xin)