Yadda kananan yara suke wasa da wayar salula yayin cin abinci kan kara musu samun kiba
2024-11-24 17:01:31 CMG Hausa
Masu nazari da suka fito daga kasashen Turai sun gano cewa, idan kananan yara su kan yi amfani da wasu na’urorin laturoni yayin da suke cin abinci, alal misali, yin wasa da wayar salula, ko kuma kallon telebijin, hadarin karuwar nauyin jikinsu da ya wuce misali zai karu.
Jaridar The Times ta kasar Ingila ya ruwaito a kwanan baya cewa, nazari mai ruwa da tsaki ya shafi ‘yan makarantar firamare dari 7 da 35 masu shekaru tsakanin 6 zuwa 10. Masu nazarin sun yi wa wadannan yara da kuma iyayensu tambaya dangane da yadda suka ci abinci cikin awoyi 24 da suka gabata, da kara sanin ko yaran sun samu damar kallon telebijin da wayar salula da sauran na’urorin laturoni yayin da suke cin abinci. Daga bisani kuma, sun yi la’akari da nauyin jikin wadannan yara, sun amince cewa, idan yara su kan yi amfani da wasu na’urorin laturoni yayin da suke cin abinci, alal misali, yin wasa da wayar salula, ko kuma kallon telebijin, hadarin karuwar nauyin jikinsu da ya wuce misali zai karu. Masu nazarin sun gano cewa, barazanar da yaran da su kan kalli na’urorin laturoni suke fuskanta ya fi wadanda ba sa kallon na’urorin laturoni yawa har da kashi 15 cikin kashi 100. Duk da la’akari da matsayinsu a zamantakewar al’ummar kasa da kuma kudin shiga, masu nazarin sun amince cewa, idan yara su kan yi amfani da wasu na’urorin laturoni yayin da suke cin abinci, hadarin karuwar nauyin jikinsu da ya wuce misali zai karu.
Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, watakila irin wannan alaka yana da nasaba da yadda kananan yara ba su mai da hankali sosai kan cin abinci sakamakon kallon na’urorin laturoni. Yayin da kananan yara suke cin abinci suna kuma kallon telebijin ko wayar salula, da wuya ne su fahimci cewa, sun riga sun koshi, don haka ba su san cewa, suna bukatar daina cin abinci ba.
Dangane da sakamakon nazarin, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin haske da cewa, wajibi ne iyaye su taimakawa ‘ya’yansu fito da kyakkyawar al’adar cin abinci, kar su yi wasa da wayar salula ko kallon telebijin yayin da suke cin abinci, ya kamata su mai da hankali kan cin abinci. (Tasallah Yuan)