Yaran da suka fi wasa kwakwalwarsu sun fi samun damar kaucewa barazanar tara kiba
2024-11-24 17:07:01 CMG Hausa
A lokacin yaranta, kwakwalwar kananan yara kan yi amfani da kuzari da yawa, yayin da nauyinsu ya karu sannu a hankali. Dalilin da ya sa mutane suka tara kiba shi ne domin abubuwan da suka ci ya fi kuzarin da suka yi amfani da shi. Don haka masu nazari da suka fito daga kasar Amurka sun gabatar da wani ra’ayi na cewa, akwai wata alaka a tsakanin yadda ake wasa kwakwalwa da barazanar tara kiba.
Masu nazari daga jami’ar Northwestern ta kasar Amurka da sauran hukumomi sun kaddamar da bayaninsu cikin jaridar kwalejin nazarin kimiyya ta Amurka, inda suka nuna cewa, idan nazarin da za su gudanar a nan gaba zai tabbatar da kasancewar irin wannan alaka, to, ma iya cewa, yadda ake ilmantar da kananan yara yana amfanawa sosai a wasu fannoni, ciki had da taimakawa kananan yara wasa kwakwalwarsu, ta yadda kananan yaran za su fi samun damar kaucewa barazanar tara kiba.
Nazarin da aka gudanar a baya ya gano cewa, kuzarin da kananan yara ‘yan shekaru 5 suke amfani da shi wajen wasa kwakwalwarsu ya kusan kai wa rabin kuzarin da suke amfani a duk jikinsu baki daya. Kana kuma, a lokacin yaranta, kananan yara sun fi amfani da kuzari wajen wasa kwakwalwarsu, yayin da saurin karuwar nauyin jikinsu ya ragu. Idan kananan yara su yi girma, to, yawan kuzarin da suke amfani da shi wajen wasa kwakwalwa yana raguwa, yayin da suka samu saurin karuwar nauyin jiki.
Don haka masu nazari sun yi hasashen cewa, sauyawar yawan kuzarin da kanana yara suka yi amfani da shi wajen wasa kwakwalwarsu tana tasiri kan yadda suka yi amfani da kuzari a jiki da kuma sauyawar nauyin jikinsu. Masu nazarin na Amurka sun yi karin bayani da cewa, ya zuwa yanzu ba a san bambancin yawan kuzarin da ko wane karamin yaro yake amfani da shi wajen wasa kwakwalwa sosai ba. Idan an auna yawan kuzarin da kananan yara suka yi amfani da shi wajen wasa kwakwalwa, to, watakila zata taimaka wajen fito da tsarin ilmantar da kananan yara, ta yadda za a amfanawa kwakwalwarsu tare da kare su daga tara kiba. (Tasallah Yuan)