Kyautata cin abinci, karatu da motsa jiki ka iya inganta kaifin basirar yara
2024-11-12 11:29:42 CMG Hausa
Kwarewar tabbatar da wani abu dangane da binciken da aka yi a kansa, yana da matukar muhimmanci wajen karatu da daidaita matsalolin da ake fuskanta a zaman yau da kullum. Wani sabon bincike ya shaida mana cewa, a cikin shekaru 2 na farko da yara suka fara karatu a makarantar firamare, yadda kananan yara suke kyautata cin abinci, kara karatu da motsa jiki kullum ka iya inganta kaifin basirar su ta fuskar tabbatar da wani abu dangane da binciken da ka yi kansa.
Masu nazari daga jami’ar Gabashin Finland, da wasu hukumomi masu ruwa da tsaki sun shafe shekaru 2 suna bibiyar ‘yan makarantar firamare na kasar Finland dari 3 da 97, ‘yan tsakanin shekaru 6 zuwa 9 a duniya, dangane da yadda suke cin abinci da kuma motsa jiki.
Masu nazarin sun gano cewa, kananan yara wadanda suke cin abinci ta hanyar da ta dace, sun fi takwarorinsu samun kaifin basira ta fuskar tabbatar da wani abu dangane da binciken da ka yi. To, ko mene ne ma’anar cin abinci ta hanyar da ta dace? Ma’anar sa ita ce kara cin ‘ya’yan itatuwa, da kayayyakin lambu, da rage cin naman sa, da sauran jan nama. Haka kuma kananan yara wadanda suka fi daukar tsawon lokaci suna karanta littattafai, da kuma motsa jiki kullum sun fi takwarorinsu samun kaifin basira ta fuskar tabbatar da wani abu dangane da binciken da ka yi. A sa’i daya kuma, kananan yara wadanda suka fi daukar tsawon lokaci fiye da kima, suna amfani da kwamfuta da kuma yin wasannin nishadantarwa kuma ba mai sa ido, suna samun raguwar kaifin basira ta fuskar tabbatar da wani abu dangane da binciken da ka yi.
Dangane da sakamakon nazarin da aka gudanar a kasar Finland, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi mana karin bayani da cewa, taimakawa kananan yara wajen kyautata cin abinci, karfafa musu gwiwa wajen karanta littattafai, da motsa jiki kullum, suna amfanar wajen kyautata kaifin basira ta fuskar tabbatar da wani abu dangane da binciken da ka yi. (Tasallah Yuan)