Illoli da fa’idoji da suke tattare da kallon na'urorin laturoni sun sha bamban tsakanin yara
2024-11-03 16:43:32 CMG Hausa
Wani nazarin da aka gudanar a kasar Australia ya nuna cewa, idan kananan yara ba sa kallon na’urorin laturoni fiye da kima, watakila yadda suke daukar tsawon lokaci suna kallon na’urorin ba ya haifar da illoli masu yawa ga dabi’arsu da ma lafiyar tunaninsu. Abu mafi muhimmanci da wajibi ne a lura shi, shi ne hanyar da suke bi wajen amfani da na’urorin laturonin da kuma abubuwan da ake nunawa kan na’urorin. Don haka illoli da fa’idojin da suke tattare da kallon na'urorin laturoni sun sha bamban tsakanin yara.
Wasu iyaye kan yi shakkar cewa, ko ya dace a bar yara su yi amfani da wayar salula da kuma tashoshin sada zumunta bisa son ransu ko a’a, ko wajibi ne a kayyade tsawon lokacin da ‘yan makarantar sakandare suke dauka wajen yin wasannin laturoni wato electronic games ko a’a. Masu nazari daga jami’ar Australian Catholic University, ko ACU a takaice sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a kwanan baya cewa, illoli da fa’idoji da suke tattare da kallon na'urorin laturoni sun sha bamban tsakanin yara. Ya kamata a yi taka tsantsan kan yanke shawara mai ruwa da tsaki.
Masu nazarin sun tantance nazarce-nazarce guda dubu 2 da dari 4 da 51 da aka gduanar a baya, wadanda suka shafi mutane miliyan 1 da dubu 900. Sun gano cewa, illoli da fa’idojin da suke tattare da kallon na’urorin laturoni ba su da yawa ga yara.
Da ma ana ganin cewa, kallon telebijin da yin wasannin laturoni sun haifar da raguwar kwarewar yara wajen yin karatu. Haka kuma karanta littattafai cikin na’urorin laturoni ko yin amfani da manhajojin ba da ilmi dukkansu sun taimakawa yara kyautata kwarewar yin karatu.
Ban da haka kuma, masu nazarin sun gano cewa, kallon na’urorin laturonin yana da nasaba da lafiyar mutane, amma kadan kadan. Alal misali, kallon talla dangane da abinci maras gina jiki a na’urorin laturoni yana da nasaba da yin sayayya ba ta hanyar da ta dace ba. Haka kuma, yadda matasa da yara suke yawan kallon telebijin ya kan haifar da raguwar tsawon lokacin barcinsu.
Ko da yake hukumar lafiya ta kasa da kasa wato WHO da kuma hukumomin gwamnatoci da dama sun ba da shawarar kayyade lokacin da matasa da kananan yara suke dauka wajen kallon na’urorin laturoni, amma nazarin da aka gudanar a Australia ya yi nuni da cewa, kallon na’urorin laturoni, batu ne mai sarkakiya. Illolin da batun ke haddasawa kan kananan yara suna da nasaba da tsawon lokacin kallon na’urorin, nau’ikan na’urorin, abubuwan da ake nunawa kan na’urorin, da yadda matasa da kananan yara suke kallo. An kau da kai daga irin wannan batu mai sarkakiya yayin da aka ba da shawarwari masu ruwa da tsaki. Masu nazarin sun yi kashedin cewa, kar a mai da hankali kan tsawon lokacin kallon na’urorin laturoni, wajibi ne a mai da hankali kan hanyoyin da ake bi wajen yin amfani da na’urorin. (Tasallah Yuan)