Mutane 1180 sun mutu a Sudan sakamakon ciwon kwalara
2024-11-27 11:26:17 CMG Hausa
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Sudan ta ba da sanarwa a jiya Talata cewa, ciwon kwalara da ya barke a sabon zagaye tun daga watan Yulin bana ya haddasa mutuwar mutane 1180.
Sanarwar ta ce, rahoton da aka gabatar na nuna cewa, a kwanaki 3 da suka gabata, karin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 253, inda daya daga cikinsu ya mutu, sannan ya zuwa ranar 26 ga wata, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 42725, daga cikinsu mutane 1180 daga yankuna 81 na jihohi 11 sun rasa rayukansu.
Sanarwar ta kuma ce, a kwanan baya, rikicin da ya barke a jihar Gezira da Sennar dake tsakar kasar ya kara tsananta, jama’a sun gudu zuwa wasu wurare, matakin da ya sa da wuya a iya magance annobar.
Har ila yau, an fi samu karin mutanen da suka kamu da cutar a jihar Gedaref da ta Kassala dake gabashin kasar da jihar River Nile dake arewa. Wadannan jihohi sun karbi karin mutanen da suka rasa gidajensu har kimanin dubu 400 da suka gudu daga yankin tsakar kasar.
Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar tana fesa ruwan kashe kwayoyin cuta da kafa cibiyar killacewa da sauransu don magance matsalar, sai dai ana bukatar karin magunguna da tallafin jinya. (Amina Xu)