logo

HAUSA

Shugabar Mexico: Barazana da matsa lambar haraji da Amurka ke yi ba za su warware matsalar makaurata da masu miyagun kwayoyi ba

2024-11-27 12:35:46 CMG Hausa

 

Shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum Pardo ta bayyana a jiya Talata cewa, matakin kawo barazana da matsa lamabar haraji da Amurka ke yi a kan sauran kasashe, su kadai ba za su warware matsalar makaurata ta barauniyar hanya da sassauta harkallar miyagun kwayoyi a cikin Amurka ba.

Ta ce, makaman dake shiga Mexico daga Amurka ta barauniyar hanya na kara tsananta har ta kai ga kashi 70 cikin dari na yawan makaman da hukumar dakile makamai ta kwace daga Amurka da aka shigo da su.

Game da batun harajin kwastam, ta ce, idan Amurka ta kara dora wa kasarta haraji, Mexico za ta dauki matakin mai da martani. Matakin da zai kara kawo wa kamfanonin kasashen biyu dimbin kalubaloli, a sa’i daya kuma zai haifar da hauhawar farashin kaya da rasa guraben aikin yi. Duba da haka ta yi kira da a yi shawarwari don tabbatar da kara fahimtar juna da zaman lafiya da wadata a tsakanin kasashen biyu.

An labarta cewa, Donald Trump ya wallafa sako a shafinsa na sada zumunta a ranar 25 ga wata cewa, daga lokacin da ya kama aikinsa na shugaban kasar Amurka a wa’adi na biyu, nan da nan zai kara haraji da kashi 25 cikin dari a kan hajojin da za a shigo da su daga kasashen Mexico da Canada, har sai an kusan kawo karshen matsalar miyagun kwayoyi da makaurata ta barauniyar hanya. (Amina Xu)