logo

HAUSA

Isra’ila ta amince da tsagaita wuta tsakaninta da Hezbollah daga safiyar Laraba

2024-11-27 10:02:46 CMG Hausa

 

Majalisar tsaron Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin kasar da kungiyar Hezbollah, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin firaministan Isra’ila ta bayyana a ranar Talata da dare.

Gidan talabijin na gwamnatin Isra’ila na Kan TV News ya ba da rahoton cewa, yarjejeniyar tsagaita bude wutar wadda Amurka da Faransa suka tsara, za ta fara aiki daga ranar Laraba da karfe 4 na asuba a yankin Isra’ilar da Lebanon.

Sanarwar ta kara da cewa, “Isra’ila tana godiya da irin gudunmawar da Amurka ta bayar har aka cimma yarjejeniyar, amma kuma tana da ‘yancin fatali da duk wani abu da zai zama barazana ga tsaronta”.

A wani jawabi da ya gabatar ta bidiyo kafin amincewa da yarjejeniyar a ranar, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce, za a amince da shawarar tsagaita bude wutar ce bisa sharuda guda uku, da farko a mayar da hankali a kan barazanar da Iran ke yi, sai bukatar kara wa dakarunsu kaimi da karin tanadin makamai, kana da zakulo ‘yan kungiyar Hamas daga zirin Gaza. (Abdulrazaq Yahuza Jere)