Najeriya da Bankin Duniya sun kulla yarjejeniyar yin hadin gwiwar bunkasa aikin noman rani da kuma samar da wuta a kasar
2024-11-27 09:21:37 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun ma’aikatatun ruwa da tsaftar muhalli da kuma na wutan lantarki sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da bankin duniya domin aiwatar da aikin noman rani da kuma samar da wuta a jihohi 25 na kasar.
An sanya hannun ne jiya Talata 26 ga wata a birnin Abuja a wani bikin da ya samu halartar ministan ruwa da tsaftar muhalli Farfesa Joseph Utsev da takwaransa na wutan lantarki Mr. Adebayo Adelabu.
Daga tarayyar Najeriya wkailinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Za a yi amfani da wadannan kudade ne domin alkintan madatsun ruwan kasar ta yadda za a iya amfani da su wajen aikin noman rani da kuma samar da wuta a wasu jihohi 25 na kasar.
A jawabinsa yayin sanya hannun ministan ruwa na tarayyar Najeriya ya bayyana aikin a matsayin wani mataki na bunkasa sha’anin samar da abinci da ayyukan yi da kuma karfafa tattalin arzikin kasa.
Shi kuwa ministan wutan lantarki Mr Adebayo Adelabu cewa ya yi wannan alaka tana da matukar muhimmancin gaske wajen inganta harkokin samar da wuta ta amfani da ruwa a kasar, lamarin da ya ce babu shakka shirin idan ya tabbata Najeriya za ta sami karin karfin wuta sosai.(Garba Abdullahi Bagwai)