Mutane 6 sun mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai a tsakiyar tashar jiragen ruwan Syria
2024-11-27 15:35:18 CMG Hausa
A yau Laraba rundunar sojan kasar Syria ta fitar da sanarwar cewa, tashar jiragen ruwa da ke makwabtaka da kasar Lebanon a yammacin lardin Homs da ke tsakiyar kasar Syria, ta fuskanci wani hari ta sama da Isra’ila ta kai a wannan rana, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 6 da jikkata wasu 12. (Bilkisu)