Jihar Niger ta Najeriya ta hada hannu da wani fitaccen kamfanin sarrafa kayan gona na kasar Sin domin rage asarar da manoman jihar ke yi
2024-11-27 09:30:43 CMG Hausa
A wani mataki na habaka sha’anin noma da kuma rage asarar dake biyo bayan girbin amfanin gona, gwamnatin jihar Niger ta hada hannu da wani kwararren kamfanin sarrafa kayan amfanin gona dake Chengdu a lardin Sichuan na kasar Sin.
Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Usman ne ya tabbatar da hakan jiya Talata 26 ga wata a Mina lokacin da yake zatawa da manema labarai bayan ziyarar da jami’an gwamnatin jihar suka kai kasar Sin.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Alhaji Abubakar Usman ya ce, suna da kwarin gwiwar cewa hada karfi da wannan kamfani zai bunkasa harkar samar da abinci a jihar, sannan kuma zai rage talauci tare kuma da inganta rayuwar al’umar jihar ta Niger.
Sakataren gwamnatin jihar ta Niger ya ce, shi ne ya jagoranci ayarin gwamnatin domin duba nau’ikan kayayyakin dake cibiyar sarrafa kayan gona dake Chengdu da Mianyang da birnin Deyang duka da suke a lardin Sichaun.
Ya ce, babban makasudin ziyarar shi ne domin a tsara yadda za a rinka musayar ilimi da fasaha da samar da damarmakin zuba jari.
Alhaji Abubakar Usman ya sanar da cewa, tuni gwamnatin jihar Niger ta amince da dukkan sharudodin da aka gindaya karkashin wannan yarjejeniya wanda kuma ya baiwa jihar damar assasa cibiya ta musamman na sarrafa kayan gona a jihar Niger ta hanyar hadin gwiwa da kwararrun na kasar China. (Garba Abdullahi Bagwai)