Sabon faraministan kasar Mali ya gana da mambobin gwamnatinsa
2024-11-26 10:49:37 CMG Hausa
A sanyin safiyar ranar jiya Litinin 25 ga watan Nuwamban shekarar 2024, sabon faraministan kasar Mali, janar Abdoulaye ya gana da masu bada shawara na musamman, kwararru, masu kula da harkokin tafiye-tafiye, mambobin majalisar na fararen hula da na majalisar sojoji dake fadar faraminista.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana rahoto daga birnin ya kai.
A yayin wannan ganawa, shugaban gwamnatin Mali, ya yi jawabi da sunan shugaban kasa janar Assimi Goita, ya kawo yabo ga mambobin fadar bisa ga jan namijin aikin da suka yi a karkashin jagorancin tsohon faraminista, dokta Choguel Maiga bayan an sallame shi daga mukaminsa na faraministan kasar Mali.
Shugaban gwamnatin kasar mai ci na yanzu, Abdoulaye Maiga, ya kara bayyana tare da jaddada cewa niyyarmu domin kasar Mali tana nan ba ta canja ba, babu canja alkibla, amma akwai 'yan gyare-gyare da za'a gudanar, babban burin shi ne na rike hanyar da aka sanya gaba domin cimma maradun kasa da tabbatar da hangen shugaban rikon kwarya Assimi Goita, mai taken Mali kura.
Sabon shugaban gwamnatin kasar Mali, ya bayyana wasu matakai da ya dauka na gaggawa da suka shafi wasu nade-nade na jami'ai, da shugaban tsofuwar gwamnati ya yi, an soke su, tare da maye gurbinsu da wasu sabbin jami'ai ta yadda tafiya za ta dore daga inda ake aza, in ji faraminista Abdoulaye Maiga.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.