logo

HAUSA

A kalla mutane 30 ne aka hallaka yayin wani sabon farmaki da ya faru a jihar Benue

2024-11-26 10:43:33 CMG Hausa

A kalla mutane 30 ne suka mutu sakamakon hare-haren da wasu ’yan ta’adda dauke da muggan makamai suka kaiwa wasu yankunan kananan hukumomi biyu a jihar Benue dake arewa ta tsakiyar Najeriya.

Maharan dai da ake zargin sun shigo ne daga wasu kasashe makwafta kuma sun shafe sa’o’i suna kai hare-hare a kananan hukumomin Katsina Ala da Logo tun daga daren Lahadi 24 ga wata zuwa wayewar garin jiya Litinin 25 ga wata.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi, shugaban majalissar karamar hukumar Katsina-Ala Justine Shaku ya ce, an tsinci gawarwakin mutane 10 a yankinsa yayin da kuma aka lalata kaddarori da dama bayan munanan raunuka da wasu suka ji sakamakon harin.

Ya ce, ’yan bindigar wanda adadinsu ya haura dari 3 sun kutso kai wasu yankuna na karamar hukumar dauke da makamai da sanyin safiyar Lahadi.

Shugaban karamar hukumar ya ce, tun da farko sai dai jami’an tsaro suka yi kokarin korar su, amma sabo da yawan da suke da shi abun ya faskara, sai daga baya aka turo sojin sama inda nan take suka fatattake su.

Shi ma shugaban majalissar karamar hukumar Logo Mr Clement Kav ya ce, maharan sun kashe mutane 20 sannan kuma sun jikkata 37 a yankinsa, inda ya tabbatar da cewa, tuni dai gwamnan jihar ta Benue ya turo jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar ta Benue Catherine Anene ta tabbatar da faruwar wannnan al’amari, amma ta ce, ya zuwa yammacin jiya Litinin gawarwarki biyar ne aka iya tantancewa a yankin karamar hukumar ta Logo. (Garba Abdullahi Bagwai)