logo

HAUSA

Rasha za ta yi amfani da makamai masu linzami matukar ta ga na Amurka a Asiya

2024-11-26 09:54:46 CMG Hausa



Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov ya bayyana cewa, kasar tana duba yiwuwar amfani da makamai masu linzami masu cin karami da matsakaicin zango a yankin Asiya matukar ta ga na Amurka yana karakaina a yankin.

Wata kafar yada labarai ta cikin gida ta ruwaito jami’in yana bayyana haka a jiya Litinin.

A lokacin da ‘yan jarida suka tambayi Sergia Ryabkov ko Rasha na duba yiwuwar amfani da makami mai linzami da ke cin karami da matsakaicin zango, ya ba da amsar cewa, “Bayyanar irin wannan makamin na Amurka a kowane yanki a duniya zai yanke hukuncin irin matakin da ya kamata mu dauka, ciki har da tsara mayar da martani na soja.”

Jami’in ya kuma ce, matukar yaki ya barke, Rasha za ta kai farmaki har a sansanonin sojin Amurka da ke yankin Turai, ciki har da wuraren da take da makaman nukiliya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)