logo

HAUSA

Labarin wani dan kasar Madagascar da ya shafi China

2024-11-26 17:04:16 CMG Hausa

Shekaru da dama da suka gabata, lokacin da wani matashi dan asalin kasar Madagascar mai suna RAKOTOARIVONY Mamisoa ke karatun Sinanci a garinsu, bai taba tunanin cewa zai samu damar zuwa kasar Sin ba, balle ma ya zama mai matukar son wasannin kwaikwayon gargajiyar kasar Sin. A halin yanzu, Mamisoa yana koyar da harshen Madagascar a jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing dake kasar Sin. Yayin da yake bitar labarinsa da kasar Sin, Mamisoa ya bayyana cewa, labarinsa ya shaida zurfin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. A cikin shirinmu na yau, bari mu ji labarin wannan matashi dan kasar Madagascar a kasar Sin.