logo

HAUSA

Ghana za ta gudanar da zabe na musammam kafin ranar babban zaben kasar

2024-11-26 10:06:24 CMG Hausa

 

Za a gudanar da zabe na musammam a wasu zababbun rumfunan zabe a fadin kasar Ghana, a ranar 2 ga watan Disamba, domin masu kada kuri’a kafin babban zabe.

Mataimakin kwamishinan hukumar zabe ta kasar Bossman Asare ne ya sanar da hakan jiya Litinin, inda ya ce za a bude wasu rumfunan zabe 328 dake fadin kasar ga masu kada kuri’a da wuri, domin su tabbatar da ‘yancinsu na kada kuri’a, kuma kowacce rumfa ba za ta karbi adadin masu kada kuri’a sama da 750 ba, domin tabbatar da aikin ya gudana ba tare da tangarda ba.

Hukumar ta bukaci mutanen da sunanyensu ke cikin jerin masu kada kuri’a da wuri, su fita a ranar zaben su kada kuri’a, domin ba za su samu wannan dama yayin babban zaben kasar ba. Ta kuma tabbatarwa masu kada kuri’ar cewa, ta dauki dukkan matakan da suka wajaba na tabbatar da an gudanar da zaben cikin adalci da lumana.

Al’ummar Ghana za ta kada kuri’ar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki 276 ne a ranar 7 ga watan Disamban bana. (Fa’iza Mustapha)