Baje kolin na’urar binciken teku
2024-11-26 08:40:48 CMG Hausa
An kaddamar da bikin baje kolin na’urorin binciken teku karo na biyu na kasar Sin na shekarar 2024 a birnin Fuzhou, fadar mulkin lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar, inda aka samu halartar shahararrun kamfanoni da jami’o’i da cibiyoyin nazarin kimiyya kusan 800. (Jamila)