logo

HAUSA

Wakilin Sin: Hawa kujerar na ki da Amurka ta yi ya haifar da cikas ga burin tsagaita wuta a Gaza

2024-11-26 10:49:40 CMG Hausa

 

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya koka game da yadda a makon jiya, Amurka ta sake hawa kujerar na ki game da yunkurin da aka yi na gaggauta dakatar da bude wuta a Gaza, lamarin da ya mayar da hannun agogo baya a yunkurin kwamitin tsaron MDD, tare da baiwa tashin hankalin dake wakana damar ci gaba da habaka.

Da safiyar jiya Litinin ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da zama game da rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda Fu Cong ya sake jaddada damuwa, game da yadda gazawar cimma nasarar burin kwamitin tsaron MDD ke nufin dorewar jinkiri, da karuwar salwantar rayukan fararen hula. Don haka a cewarsa, wajibi ne a ingiza matakan gaggawa, ba tare da gindaya sharadi ba, da tabbatar da dakatar da bude wuta mai dorewa, da kawar da duk wasu shingaye dake dakile shigar da agajin jin kai, da kin amincewa da matakan kashin kai na bangare guda, wadanda ke yin zagon-kasa ga manufar kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, da dakile kara fadadar rikicin Gaza zuwa karin sassan yankin.

Fu, ya kuma yi kira ga daidaikun kasashe da su fuskanci nauyin dake wuyansu, su taimakawa kwamitin tsaron MDD wajen cimma nasarar amfani da dukkanin hanyoyi, na kaiwa ga dakatar da bude wuta da dawo da zaman lafiya a Gaza.  (Saminu Alhassan)