logo

HAUSA

Labarin Jiang Fengzhen na samar da shinkafa mai inganci

2024-11-25 22:25:46 CMG Hausa

Jiang Zhenfeng data fito daga dangin karkara a gundumar Jianghua mai cin gashin kanta ta kabilar Yao a birnin Yongzhou na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Lokacin da take karama, duk hutun lokacin zafi da na bazara, ta kan bi mahaifiyarta tashar hatsi kuma ta ki barinta.

A shekarar 2003, Jiang Zhenfeng ta tafi lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin don yin aiki, inda aka fallasa ta ga manufar “abinci mai tsabta”, wadda ta sa ta fito da ra’ayin komawa garinsu don fara kasuwanci.

Bayan ta koma garinsu kuma, Jiang Zhenfeng ta kafa wata masana’antar gyaran hatsi. Amma sakamakon rashin daidaito na ingancin shinkafar da suka saya, ba su iya sayar da shinkafa yadda ya kamata ba, don haka ta yanke shawarar shuka shinkafa da kanta.

Ba kamar yadda aka saba yi ba, ta dauki hanyar shuke-shuke ta kare halittu, ta dage kan rashin amfani da magungunan kashe kwari, da kau da ciyayi da hannu.

A cikin shekara ta farko, ruwan sama mai yawa da ba kasafai ake fama da shi ba, da kuma bayyanar katantanwa a cikin gonaki, sun haifar da raguwar noman shinkafa da hasarar dimbin yawa.

A cikin shekara ta biyu, Jiang Zhenfeng ta koyi darasi da goggagu da ta yi a baya, kuma ta samu girbin shinkafa mai yawa. Amma, saboda kudin da aka kashe wajen shuka shinkafa, da farashin shinkafa duk sun yi yawa, da kuma babban matsayin shinkafa da aka tabbatar, babu mutane da yawa ke son sayensu, hakan aka gamu da matsalar sayar da shikafa.

Amma wadanda ba su yin watsi da fatan da suke son cimmawa ba, za su iya samun sakamako mai kyau.

A shekarar 2014, da sanin cewa akwai damar halartar bikin baje kolin aikin gona na tsakiyar kasar Sin a birnin Changsha na lardin Hunan, Jiang Zhenfeng ta garzaya zuwa wurin da tawagarta ba tare da wata shakka ba.

A wajen baje kolin, ita da ’yan tawagarta sun tuhumi shinkafar da suka shuka, tare da ba wa mahalartan da ke wucewa ta rumfar su don dandana. Shinkafa mai dadi da kamshi ta samu karbuwa a wajen kowa da kowa, sannan kuma ya taimakawa Jiang Zhenfeng wajen samun kasuwa da tallace-tallace na sayar da shinkafa.

Shinkafa mai inganci da ta shuka tun daga lokacin, ta shiga matsakaici da kananan kantuna da shaguna, da wuraren haihuwa, da gidajen cin abinci masu tsada, har ma ta fita daga lardin Hunan zuwa duk fadin kasar ta Sin.

Da take waiwayen baya kan yadda take gudanar da kasuwanci a matakin farko, Jiang Zhenfeng na ganin cewa, wannan abu ne mai daraja ta rayuwarta. Ta ce, “Idan mutum bai shiga wani mawuyacin hali mai tsanani ba, ba zai iya bayyana boyayyen karfinsa kwata kwata ba.”

Jiang Zhenfeng ta san cewa ba tana noman shinkafa mai inganci kawai don rayuwa ba ne, har ma ya kasance alhaki da nauyin dake bisa wuyanta. Tana son ta zarce magabata ta hanyar kirkire-kirkire, da kuma kyautata shinkafar da ta shuka, don samun damar fito da shinkafar daga tsaunuka masu zurfi, tare kuma da sanya mutane da yawa su dandana shinkafa mai kamshi da aka shuka a wurin.

Jiang Zhenfeng ta fara bullo da sabbin fasahohin aikin gona da na’urorin samar da kaya na zamani, tare da kokarin yin aiki mai kyau ta kowane fanni tun daga shuki har zuwa girbi. A ganinta, dole ne shugaba ya yi hangen nesa kan ci gaban masana’antarsa, in ba haka ba, masana’antar za ta rasa karfin yin takara.

Baya ga haka kuma, Jiang Zhenfeng ta yi cikakken nazarin al’adun gargajiya da halayen al’adu na wurin, kuma ta dauki gajeren bidiyo, don baje kolin tufafi irin na kabilar Yao, abinci masu dadi da yadda suke shukar shinkafa, da ma yanayin halittu na garinsu a dandalin sada zumunta na yanar gizo. A sa’i daya kuma, ta hanyar shirya gasar yawon bude ido a yankunan karkara kamar dashen dashen shinkafa, da yankan shinkafa, da kamun kifi, shinkafar da suke nomawa ta kara samun karbuwa a wajen masu sayayya, kuma tallace-tallace na ci gaba da karuwa.

A halin yanzu, sannu a hankali mafarkin Jiang Zhenfeng yana zama gaskiya, kuma ana fitar da shinkafa mai inganci na kamfaninta zuwa birane sama da 230 na larduna 26 na kasar ta Sin.

Jiang Zhenfeng ta ce, “Kayayyakinmu sun fito ne daga tsaunuka masu zurfi, don haka akwai wuyar a kai su zuwa sauran yankuna, amma duk da haka muna kokarin samar da kaya bisa odar da aka yi cikin sa’o’i 24.” Ta kara da cewa, nan gaba kuma za ta kara kokarinta na kyautata hidimar jigilar kayayyaki.

A watan Nuwamba na shekarar 2021, an fara aiwatar da sabbin ka’idojin sana’ar shinkafa ta kasar Sin a hukumance, inda kuma kamfanin Jiang Zhenfeng ya hada kai tare da cibiyar nazarin shinkafa na kasar Sin, da cibiyar nazarin samar da abinci masu tsabta ta kasar dama sauran hukumomin da yawansu ya kai shida, sun tsara takardun da batun ya shafa, ta yadda Jiang Zhenfeng ta zama daya daga cikin masu tsara takardun ka’idoji guda 14.

A matsayinta na ’yar manomi, Jiang Zhenfeng a ko da yaushe tana kulawa da garinsu sosai, tana mayar da tallafawa manoma wajen kawar da talauci da samu wadata a matsayin ginshikin ci gaban kamfaninta. Kamfaninta na amfani da wani tsarin gudanarwa irin na masana’antar da aikin gona, wato a gudanar da hadin kai a tsakanin kamfani, da kungiyar hadin kai da kuma manoma, inda za a samar da iri da taki da kuma fasaha ga manoman da suke bin tsarin hadin gwiwar, ta hakan aka jagoranci manoma sama da dubu 80 don raya sana’ar shinkafa irin na kiyaye muhalli, ta yadda suka tabbatar da kara samun kudin shiga, har ma da kawar da talauci da samun wadata.

Jiang Zhenfeng ta ce, “Yanzu muna cikin zamani mafi kyau, wanda ya samar da mafi kyawun dama ga mu mata don mu yi aiki da ma gudanar da kasuwancinmu. A nan gaba, za mu ci gaba da kara zuba jari a fannin fasaha, da samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire, kana da yin amfani da fasahohin da za su taimaka wa manoma su samu karuwar shinkafa masu inganci da suke nomawa, don ba da gudummawa ga samar da isasshen abinci ga kasa, da kuma farfado da yankunan karkara gaba daya a kasar.”