logo

HAUSA

Manzon musamman na babban sakataren MDD ya yi kiran kauce wa jefa Syria cikin rikicin gabas ta tsakiya

2024-11-25 14:26:09 CMG Hausa

Manzon musamman na babban sakataren MDD kan batun Syria, Geir Otto Pedersen ya yi kira a Damascus, babban birnin Syria a jiya Lahadi cewa, ya kamata kasashen duniya su dauki matakai don saukaka yanayin tashin hankali na Gabas ta Tsakiya, tare da kauce wa jefa Syria cikin rikicin yankin.

A hirar da Pedersen ya yi da kafofin watsa labarai a jiya bayan da ya gana da ministan ma’aikatar harkokin waje da kula da 'yan kasar Syria dake zama a ketare Bassam Sabbagh, ya bayyana cewa, kawo karshen rikicin dake Lebanon da zirin Gaza na Falasdinu yana da muhimmanci sosai. Kwanan baya, ’yan Syria fiye da dubu 400 sun koma kasar daga Lebanon don gudun yaki, kuma wannan babban nauyi ne ga gwamnatin Syria da al’ummar kasa da kasa.

Pedersen ya kara da cewa, a halin yanzu, Syria tana fuskantar kalubale daban daban, don haka ana bukatar daukar dukkanin matakai don maido da kwanciyar hankali, wadanda suka hada da daidaita matsalolin Syria kamar yanayin siyasa, yanayin tsaro, maido da ikon mulkin kasar da ’yancin kanta, farfado da tattalin arziki, kawo karshen takunkumi, sake ginawa da kuma kula da ’yan gudun hijira. Ya yi kira ga kasashen duniya da su kara tallafa wa Syria a cikin wannan mawuyacin hali. (Safiyah Ma)