Sojojin gwamnatin Kamaru sun hallaka ‘yan aware biyu a arewa maso yammacin kasar
2024-11-25 10:47:32 CMG Hausa
Sojojin gwamnatin kasar Kamaru sun hallaka wasu ‘yan aware su biyu, ciki har da kwamandan mayakan, yayin wani farmaki da suka kai maboyarsu dake birnin Bamenda na arewa maso yammacin kasar.
Wani jami’in soji da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, sojojin gwamnatin Kamarun sun farmaki ‘yan awaren ne da sanyin safiyar jiya Lahadi, inda suka yi nasarar hallaka mutane biyu, ciki har da kwamandansu da ya jima yana addabar al’umma, ta hanyar yin garkuwa da mutane da neman dumbin kudin fansa. Kaza lika, ya hallaka sojoji da fararen hula masu tarin yawa. (Saminu Alhassan)