logo

HAUSA

Najeriya ta ce tana daf da sanya hannu kan yarjejeniyar soji da kasar Saudiya

2024-11-25 10:41:23 CMG Hausa

Karamin ministan tsaro na tarayyar Najeriya Dr. Bello Mohammed Matawalle ya tabbatar da cewa, Najeriya na daf da kulla yarjejeniyar soji da kasar Saudiya wadda za ta kunshi shirya bayar da horon hadin gwiwa da sauran shirye-shiryen yaki da ’yan ta’adda da kuma musayar bayanan sirri.

Ya tabbatar da hakan ne a karshen mako yayin wata ganawar da ya yi da ministan tsaron Saudiya Prince Khlaid Bin Salma a birnin Riyadh.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kamar dai yadda yake kunshe cikin wata sanarwar da ta fito daga ma’aikatar tsaro ta Najeriya wadda kuma aka rabawa manema labarai a birnin Abuja, Dr Bello Mohammed Matawalle ya ce, ziyarar da ya kai kasar ta Saudiya ya yi ta ne da nufin kara karfafa alakar hadin gwiwa tsakanin rundunar sojin Najeriya da kuma takwararta ta kasar Saudiya.

Ya shaidawa ministan tsaron na Saudiya cewa, Najeriya ta gamsu da irin rawar da kasar ta Saudiya ke takawa wajen tabbatar da tsaro a shiyyar gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya, a don haka ya yi fatan cewa ziyarar tasa za ta samar da sabbin damarmaki na karfafa mu’amala ta hadin gwiwa domin shawo abubuwan dake haifar da barazanar tsaro a Najeriya, inda ya ce, za a cimma wannan buri ne kawai ta hanyar tarukan hadin gwiwa domin karfafa kwazon dakarun sojin na Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)