logo

HAUSA

MDD na bukatar karin tallafin gudanar da ayyukan jin kai a Sudan a shekarar 2025

2024-11-25 10:22:12 CMG Hausa

Sabon mataimakin babban magatakardar MDD game da ayyukan jin kai da tsare-tsaren ayyukan gaggawa mista Tom Fletcher, ya ce MDD na aiki tare da gwamnatin kasar Sudan, don ganin an samar da karin kudaden aiwatar da abubuwan da aka tsara, na tallafin jin kai a Sudan a shekarar 2025 dake tafe.

Kamfanin dillancin labarai na Sudan ko SUNA, ya ce mista Fletcher ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin ganawarsa da shugabar hukumar lura da ayyukan jin kai ta kasar Sudan Mona Nourel Daim a birnin Port Sudan. Mista Fletcher wanda ya kai ziyarar gani da ido birnin na Port Sudan, ya jaddada bukatar hada karfi da karfe wajen dakile sake tabarbarewar rikicin Sudan. Ya ce "Za mu yi aiki tare da gwamnatin Sudan, don ganin an samar da karin kudaden gudanar da agajin jin kai a Sudan a shekarar 2025."

Mista Fletcher ya ziyarci Port Sudan a karon farko bayan kama aiki a ranar 18 ga watan nan na Nuwamba. Ya kuma bayyana ziyarar ta sa a matsayin wata dama ta nazartar halin jin kai a zahiri, tare da zantawa kai tsaye, tare da wadanda tashe tashen hankula suka shafa a kasar ta Sudan. (Saminu Alhassan)