logo

HAUSA

Taron majalissar zartaswar Najeriya ya amince da kasafin naira tiriliyan 4 ga hukumomin raya shiyoyin kasar

2024-11-25 10:14:28 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya a karon farko ta amince da kasafin kudi na naira tiriliyan 4 ga hukumomin raya shiyoyin kasar, za a yi amfani da kudaden ne wajen aiwatar da ayyukan raya kasa a wuraren da aka bari a baya wajen ci gaba.

An tabbatar da hakan ne a karshen mako yayin taron majalissar zartaswa ta kasa wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a birnin Abuja. Shiyoyin da za su kasafta wadannan kudade sun hada da hukumar raya shiyyar arewa maso gabas da hukumar raya yankin Niger Delta da hukumar raya yankunan arewa ta tsakiya da kuma sauran shiyoyin da suke bukatar agajin musamman.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Bangarorin da kasafin kudin zai baiwa fifiko sun hada da samar da wutar lantarki da gyaran titunan mota da gadoji da tallafawa rayuwar mutanen da suke zaune a matsugunan ’yan gudun hijira da samar da ayyukan yi ga al’umomin da suke a yankunan da tashe-tashen hankula ya shafa.

Sauran bangarorin da za a mayar da hankali a kansu su ne inganta sha’anin kiwon lafiya, ilimi da kuma bayar da horon dogaro da kai.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, ministan kudi na tarayyar Najeriya Mr. Wale Edun ya ce, kasafin kudin zai taimaka wajen tabbatar da adalci a harkar rabon arzikin kasa tare kuma da kawo karshen dadewar da wasu bangarorin suka yi ba tare da samun ayyukan ci gaba ba. (Garba Abdullahi Bagwai)