Gwamnan jihar Borno ya kawo shawarar da a yi garanbawul a harkar ilimi domin ya dace da bukatun masana’antu
2024-11-24 15:00:04 CMG Hausa
Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum ya kawo shawarar da a sake fasalta tsarin ilimi a kasar domin ya dace da bukatun masana’antu, ta yadda za a rinka yaye daliban da suka samu kwarewa a dukkan fannonin da suke da nasaba da ayyukan kamfanoni.
Ya bayar da shawarar ce a ranar Jumma’a ranar 22 ga wata a Maiduguri, fadar gwamnatin jihar lokacin da yake karbar bakuncin manajan daraktan asusun bada rancen kudin karatu ga dalibai a Najeriya Mr. Akintunde Sawyerr.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Farfesa Babagana Umaru Zulum ya bayyana damuwa bisa yadda da yawa daga cikin daliban da manyan makarantu a Najeriya ke yayewa ba su da wata kwarewa a fannin kirkire-kirkire da fasahar kere-kere.
A saboda haka gwamnan na jihar Borno ya yi kira ga asusun da ya duba yiwuwar samar da mafita a kan yadda daliban Najeriya za su kasance masu dogaro da kansu maimakon sanya ransu wajen neman aiki a gwamnatoci da wasu hukumomi.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, akwai matukar bukatar a rinka samun tuntubar juna a tsakanin makarantu da kuma masana’antu domin samun damar yaye dalibai da kamfanoni ke bukatar aikin su.
Gwamnan na jihar Borno ya ce, baya ga bayar da rance ga dalibai, akwai bukatar asusun ya rinka bayar da tallafi na musamman ga tsarin karatun da ake koyar da sana’o’in hannun da kuma fasahar kere-kere, inda ya ce yin hakan zai kara kwadaitar da dalibai sha’awar nazarartar irin wadannan darussa. (Garba Abdullahi Bagwai)