WHO: Mpox har yanzu matsalar lafiyar jama’a ce da ke bukatar matakin gaggawa
2024-11-23 16:28:37 CMG Hausa
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar a ranar Juma’a cewa, karuwar cutar kyandar biri na ci gaba da zama matsalar lafiyar jama’a da ke bukatar dauki na gaggawa kuma abin damuwa ga kasashen duniya.
A cikin wata sanarwa, hukumar ta WHO ta ce shawarar wacce aka yanke a taron kwamitin gaggawa na ka'idojin kiwon lafiya na duniya, ya dogara ne akan karuwar adadin da kuma ci gaba da yaduwar cutar a wurare, da kalubalen da ake fuskanta a fagen aiki, da bukatar daukar mataki mai dorewa cikin hadin gwiwa tsakanin kasashe da abokan hulda.
A watan Agusta ne dai WHO ta ayyana dokar ta-baci a fannin kiwon lafiya saboda barkewar cutar kyandar biri a Afirka. An kuma tabbatar da adadin mutane 12,596 masu dauke da cutar ya zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba, a cewar rahoton WHO. (Mohammed Yahaya)