Dan Nijeriya Lookman Na Kan Gaba Wajen Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika Ta Bana
2024-11-21 16:51:46 CRI
Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasa biyar da suka fi cancanta domin lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na shekarar 2024 a hukumance, inda dan wasan Super Eagles ta Nijeriya, Ademola Lookman ya jagoranci jerin sunayen.
A wannan jadawali da hukumar ta CAF ta fitar, kyaftin din Nijeriya Wiliam Trost Ekong bai samu damar zama daga cikin sunayen yan wasan biyar ba.
Dan kasar Cote d’Ivoire, Simon Adingra; Serhou Guirassy na Guinea; Dan wasan baya na Morocco, Achraf Hakimi, da mai tsaron gida na Afrika ta Kudu, Ronwen Williams, su ne sauran ‘yan wasa hudu da aka zaba don lashe kyautar gwarzon dan wasan CAF na bana.
Sauran nau’o’in kyaututtukan da aka sanar a ranar Litinin sun hada da Gwarzon Golan Shekara, Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Interclub, Koci Na Shekara, Gwarzon Dan Wasa Na Shekara, Gwarzuwar Kungiya da kuma gwarzuwar tawagar kwallon kafar kasa na Shekara.
Bikin mai kayatarwa akan tsara shi domin nuna irin cigaba da harkar kwallon kafa a Afrika ta samu da kuma karrama yan wasa da kungiyoyin kwallon kafa da sukafi taka rawa a shekarar da ta gabata,wanda zai kai ga lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka na CAF na bana a bangaren maza da mata.
Messi, Ronaldo, Lookman Na Cikin ‘Yan Wasan Da Ke Takarar Kyautar Globe Soccer Awards Ta Bana
An saka sunan dan wasan Nijeriya, Ademola Lookman a cikin wadanda aka zaba don samun kyautar gwarzon dan wasan maza na shekarar 2024, wanda kungiyar Globe Soccer ta ke bayarwa kuma hukumar wasanni ta Dubai ke karbar bakunci.
Globe Soccer Awards ta sanar da hakan a ranar Alhamis a wata sanarwa da ta saka a shafinta na X.
Tsohon dan wasan Leicester wanda yanzu haka tauraruwarsa ke haskawa a Atalanta ta kasar Italiya, ya yi fice a ‘yan shekarun nan tare da Atalanta a Seria A.
Lookman ya shiga cikin manyan taurarin kwallon kafa, Lionel Messi, Cristiano Ronaldo, Kylian Mbappé, da Erling Haaland na daga cikin jerin ‘yan wasan da ka iya lashe kyautar.
Dan wasan Manchester City, Phil Foden, Jude Bellingham na Real Madrid, da Cole Palmer na Chelsea suna wakiltar manyan kungiyoyin kwallon kafa na Ingila, Messi da Ronaldo sun sake fitowa a cikin jerin sunayen duk da cewar su na tunkarar shekarunsu na karshe na taka leda.
Robert Lewandowski na Barcelona da Leroy Sané na Bayern Munich, tare da Bukayo Saka, suna cikin jerin sunayen.
Globe Soccer Awards ta ce duk dan wasan da ya fi samun yawan kuri’u zai kasance a cikin jerin ‘yan wasa uku da za su shiga mataki na gaba wajen neman lashe kyautar
Nijeriya Na Buƙatar Maki 3 Yau Domin Samun Gurbi A Gasar Ƙasashen Afrika
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya a yau Alhamis za ta fafata da takwararta ta ƙasar Benin a wasan zagaye na biyar na wasannin neman gurbin buga gasar kofin ƙasashen Afrika da za a buga a ƙasar Moroco a shekarar 2025.
Nijeriya ta na matsayi na ɗaya da maki 10 yayinda ƙasar Benin ke bi mata a matsayi na 2 da maki 6, idan Nijeriya ta doke Benin a yau hakan zai ba ta damar buga gasar ƙasashen Afrika ta shekarar 2025 a Moroco.
A wasan farko da ƙasashen biyu su ka haɗu a Abuja, Nijeriya ce ta doke Benin da ci 3 da nema inda Victor Osimhen ya jefa ƙwallo ɗaya Ademola Lookman ya jefa kwallaye biyu a ragar Benin.
Pep Guardiola Ya Tsawaita Kwantiragi A Manchester City Har Zuwa Shekarar 2027
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya rattaba hannu kan tsawaita kwantiragin shekara daya, tare da zabin karin shekara guda, wanda zai iya ci gaba da rike shi har zuwa shekarar 2027, Guardiola ya taka rawar gani a tsawon lokacin da ya shafe a Etihad ya samu nasarar lashe kofunan gasar Firimiya sau hudu a jere wanda shi ne karo na farko da wani ya yi haka a tarihin kwallon kafa ta Ingila.
Labarin ya samu karbuwa sosai daga magoya baya da kuma masana harkar kwallon kafa, wadanda ke kallonsa a matsayin wani shiri na ci gaba da jagoranci a Manchester City,a karkashin jagorancin Guardiola kulob din ya samu gagarumar nasara a gida da waje,kamar nasarar cin kofin zakarun Turai a shekarar 2023.
Tsawaita zaman Guardiola ya sake tabbatar da aniyar Manchester City na yin aiki kafada da kafada da manyan mashawarta a harkar kwallon kafa wajen ganin ta cigaba da jan zarenta a harkar kwallon,wanda hakan ke kara tabbatar da su na amsa sunansu na matsayin babbar kungiyar kwallon kafa a duniya.
Har Yanzu Arsenal Ta Na Iya Lashe Gasar Firimiya Ta Bana – Alan Shearer
Shahararren dan wasan kasar Ingila Alan Shearer ya yi imanin cewa har yanzu Arsenal na iya lashe gasar Firimiya ta kasar Ingila duk da cewar akwai tazarar maki 9 tsakaninta da Liberpool wadda ke jan ragamar teburin gasar.
A ranar Lahadin da ta wuce ne Gunners din suka tashi kunnen doki 1-1 da Chelsea a Stamford Bridge, Gabriel Martinelli ne ya zura kwallo a ragar Chelsea kafin sabon dan wasan Blues din da ya zo daga Wolberhampton Wanderers a bana ya farke ma Chelsea kwallo dab da za a tashi daga wasan.
Canjaras din da ta yi na nufin Arsenal na matsayi na 4 a teburin gasar Firimiya da maki 19 a wasanni 11 da aka buga, amma Shearer, wanda ya lashe gasar Premier tare da Blackburn Robers a shekarar 1995, yana da kwarin gwiwar cewa Arsenal za ta iya ci gaba da samun nasara don rage tazarar maki.
Makin da ke tsakaninsu da Liberpool ya na da yawa amma ina ganin Arsenal za ta iya taka rawar gani sosai, ‘yan wasansu sun samu rauni makwanni biyu da suka gabata, idan su ka dawo bayan hutun kasa da kasa za su iya bayar da mamaki domin za su dawo da cikakken karfinsu domin ci gaba da taka leda inji Shearer wanda ke rike da tarihin wanda ya fi zura kwallo a tarihin gasar Firimiya.
Don haka bai kamata ayi watsi da Arsenal ba tukuna, ina tsammanin ganin sakamako mai kyau daga garesu domin kuwa su na da jagoranci mai kyau,wasa na gaba da Arsenal za ta buga shi ne wanda za ta karbi bakuncin Nottingham Forest a filin wasa na Emirates Stadium da ke birnin Landan.
Bayan wasan da Forest, za su je Portugal don karawa da Sporting Lisbon a gasar zakarun Turai,sannan su koma wasan Firimiya a gidan West Ham kafin su yi wasa da Manchester United.
Manyan Kugiyoyin Gasar Firimiya Sun Fara Zawarcin Victor Osimhen