logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kananan yara su suka fi fuskantar kalubalen talauci a kan manya a kasar

2024-11-21 09:59:22 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce, kananan yara a kasar su ne suka fi fuskantar kalubalen talauci a kan manya, saboda gaza amfana da wasu damarmaki guda 10 da suke nuna wadata a harkokin rayuwar dan adam.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki Sanata Abubakar Bagudu ne ya tabbatar da hakan jiya Laraba 20 ga wata a birnin Abuja yayin bikin ranar yara ta duniya na shekara ta 2024.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Sanata Abubakar Bagudu wanda ya yi jawabi ta bakin  babban sakatare a ma’aikatar kasafin kudi na tarayya Mr Vincent Obi, ya ce abin takaici kaso mafi yawa na kananan yaran dake Najeriya ba sa iya samun wadataccen ruwan sha, da muhalli mai kyau da nau’ikan abinci mai gina jiki da kula da lafiyarsu da kuma ingataccen ilimi wadanda dukkanninsu suna cikin jerin muhimman bukatun rayuwa guda 10.

Ministan ya ce, a yanzu haka kaso 26 na daliban makarantun firamare da kaso 25 na karamar sakandare da kuma kaso 24 na daliban babbar makarantar sakandare ba sa iya zuwa makaranta, haka kuma yara miliyan 1.3 ne aka tilasta musu barin gidajensu saboda tashe-tashen hankula.

Ministan kasafin kudin na tarayyar ya ce, a halin yanzu gwamnati ta shigar da tsarin yaki da talauci da shirye-shiryen da za su tabbatar da kariya da inganta rayuwar kananan yara cikin manufar ci gaban kasa na shekara ta 2025, baya ga wannan kuma gwamnatoci a dukkan matakai suna aikin hadin gwiwa da kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa wajen bayar da tallafin rayuwa ga kananan yara a Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)