Rahoto: Matsayin intanet na Amurka da na Sin su ne kan gaba wajen samun ci gaba a duniya
2024-11-21 13:58:52 CMG Hausa
A yau Alhamis 21 ga Nuwamba, yayin gudanar da babban taron intanet na duniya na bana na Wuzhen, Cibiyar Binciken Harkokin Intanet ta kasar Sin ta fitar da rahoton ci gaban da ake samu a bangaren intanet na shekarar 2024 da kuma rahoton ci gaban da intanet na kasar Sin ya samu duk dai a shekarar.
Rahoton mai lakabin shudin littafi ya bayyana cewa har yanzu intanet na kasar Amurka da na kasar Sin ne a kan gaba wajen samun ci gaba a duniya inda suke da maki 77.89 da kuma 69.00 bi-da-bi, kana ya ce har yanzu akwai sararin kara bunkasa sadarwar intanet a yankin tsakiyar Asiya da kuma Afirka.
Kasar Sin ita ce ta biyu a duniya a mizanin auna ci gaban intanet. Ta bangaren samar da kayan aiki na fasahar sadarwa kuwa, zuwa watan Yunin 2024, kasar Sin ta samar da fasahar sadarwar intanet mai karfin 5G, da masu wayoyin salula miliyan 889 ke amfani da ita, inda hakan yake da kaso 52 cikin dari na adadin masu amfani da 5G.
A cewar rahoton, wasu bayanai daga Hukumar Kula da Ikon Mallakar Fasaha ta Duniya sun bayyana cewa, daga shekarar 2014 zuwa 2023, kasar Sin ta gabatar da bukatar neman ikon mallakar abubuwan da aka sarrafa da fasahar kirkirarriyar basira ta AI fiye da 38,000 inda hakan ya sa ta zamo ta farko a duniya ta wannan fuskar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)