logo

HAUSA

Kasar Sin ta sake zama ta farko a duniya karo na 35 a jere a bangaren samar da kayayyakin ruwa na ci

2024-11-21 11:42:49 CMG Hausa

A jiya ne masu dauko rahoto na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) suka gano wani labari daga ma’aikatar ayyukan gona da kula da yankunan karkara cewa, aikin zamanantar da sana’ar kamun kifi na kasar Sin ya samu karin ci gaba, kuma yawan kayayyakin ruwa na ci da kasar Sin take samarwa ya sa ta sake zama kasa ta farko a karo na 35 a jere ta wannan fuskar.

Bayanai sun nunar da cewa kayayyakin ruwa na ci da kasar Sin take samarwa ya kai tan miliyan 71.16 a shekarar 2023. An samu bunkasar samar da kayayyakin ne saboda saurin ci gaban da aka samu na aikin inganta sana’ar kamun kifi na kasar Sin.

A cikin teku, kasar Sin ta gina wuraren kiwo na ruwa 169 a matakinta na cikin gida, tare da samar da ruwa na kiwo mai zurfin mita miliyan 56.6 da kuma samar da tan 470,000. A kan doron kasa kuma, an ci gaba da inganta matakan da ake amfani da su na kiwo na kandami, kuma nau'o’in kiwon kayayyakin ruwa na ci iri-iri da noman shinkafa sun bunkasa. A halin yanzu, kason kiwon kifi a cikin kayayyakin ruwa na ci da kasar Sin take samarwa ya karu zuwa matsayin 82:18, kuma yawan kiwon ya kai kusan kashi 60 a cikin dari na duniya baki daya.

Bugu da kari, kasar Sin ta samar da kyakkyawar kariya ga nau’o’in kayayyakin ruwa na ci 458 inda aka samu karin nau’o’in kayayyakin guda 410 daga shekarar 1989. (Abdulrazaq Yahuza Jere)