logo

HAUSA

Wakilin Sin ya ce abin kunya ne hawa kujerar na ki da Amurka ta yi a kan kudurin tsagaita wuta a Gaza

2024-11-21 13:40:37 CMG Hausa

A jiya Laraba, agogon Amurka ne Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a kan wani kuduri na neman tsagaita wuta a yankin Gaza wanda mambobin kwamitin marasa kujerar dindindin su 10 suka gabatar.

Ba a samu nasarar amincewa da kudurin ne ba sakamakon hawa kujerar na ki da Amurka mai kujerar dindindin ta yi.

A jawabin da ya yi bayan kada kuri’ar, babban wakilin kujerar dindindin ta kasar Sin a MDD Fu Cong ya ce, sakamakon kuri’ar da aka kada ya ba kasar Sin kunya ainun musamman yadda Amurka ta yi amfani da cikakken ikonta na hawa kujerar na ki wajen dakushe fatan da ya rage wa al’ummar Gaza na rayuwa tare da kara tura su cikin duhu da zullumi.

Fu Cong ya nunar da cewa kimanin mutum 44,000 suka mutu a Gaza amma duk da haka Amurka ta yi amfani da ikonta na hawa kujerar na ki ba tare da wata-wata ba.

Ya kara da cewa, “wai shin kisan mutum 44,000 bai isa ya sa Amurka ta ji tausayi ko kamar kwayar zarra ba a zuciyarta?” (Abdulrazaq Yahuza Jere)