logo

HAUSA

An bude taron koyar da ilimin sana’o’i na duniya na shekarar 2024 a Sin

2024-11-21 12:14:58 CMG Hausa

Yau Alhamis aka bude taron koyar da ilmin sana’o’i na duniya na shekarar 2024 a birnin Tianjin dake kasar Sin, inda wakilai 1200 daga kasashe ko yankuna fiye da 100 ke halartar taron mai taken “Kikire-kirkire na samar da makoma mai kyau, kana fasahohi na inganta zaman rayuwar Bil Adama”. Mahalarta taron za su tattauna da kuma zartas da matsaya daya na Tianjin wajen raya aikin koyar da ilmin sana’o’i a duniya, kuma za a gudanar da taruka 6 da za su shafi batun tabbatar da ingancin sha’anin koyar da ilimin sana’o’i, da manyan tsare-tsaren da duniya za ta bi wajen horas da kwararru masu fasaha, da dai sauransu, ta yadda za a kara cudanya da mu’ammala kan sabuwar hanyar da za a bi, ta fuskar hadin gwiwar kasashen duniya a bangaren koyar da ilimin sana’o’i. (Amina Xu)