logo

HAUSA

Zanga zangar neman murabus din faraminista Choguel Kokala Maiga na kasar Mali na ci gaba da kamari

2024-11-20 16:48:47 CMG Hausa

A kasar Mali wani rikicin siyasa na kokarin kunno kai, tun bayan da firaministan kasar Choguel Kokalla Maiga, ya yi kira da a tsaida jadawalin kawo karshen rikon kwarya na sojoji a yayin wani taron gamgami a ranar Asabar da ta gabata.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Tun lokacin wannan furuci na faraministan kasar Mali, Choguel Maiga, kungiyoyin fararen hula, kungiyoyin mata da na matasa, da kungiyoyin kwadago, suka nuna adawa da wannan furuci na shugaban kwamitin rikon kwarya tare da kawo goyon bayansu ga sojojin kasar a karkashin jagorancin janar Assimi Goita.

'Yan kasar Mali suka amsa kiran kungiyoyin kare mutuncin kasar Mali kamar kungiyar M5- RFP, kungiyar DCAP ta Kayes, kungiyar matan Camp na Kati, da kungiyar FPR-MALIBO, inda magoya bayansu sun fito kwansu da kwalkwata, a ranar jiya Talata 19 ga watan Nuwamban shekarar 2024, domin yin allawadai da kalaman faraminista Choguel Maiga, tare da neman da ya yi murabus. (Mamane Ada)