logo

HAUSA

Jami'in yada labarai: Kasar Sin a shirye take ta aiwatar da hadin gwiwar kasashe na hakika tare da mambobin G20

2024-11-20 09:07:00 CMG Hausa

A jiya Talata, wani jami'in yada labarai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar na fatan yin hadin gwiwa tare da sauran kasashe mambobin kungiyar G20, domin gudanar da ayyukan hadin gwiwa na hakika. Ya fadi haka ne a yayin da aka tambaye shi karin haske game da jawabin da Shugaba Xi Jinping ya yi a kan sauye-sauyen hukumomin gudanar da harkokin duniya, da ya gabatar a wurin taron kolin G20 da ake gudanarwa a Brazil.

Jami'in yada labarun Lin Jian ya ce, tun daga lokacin da aka kafa kungiyar G20, a ko da yaushe tana fuskantar kalubalen duniya gaba daya, kuma tana kokarin samar da hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya bisa tsarin tuntubar juna da cin gajiyar juna.

A cewar jami'in, a cikin jawabin da Shugaba Xi ya gabatar yayin zama na biyu na taron kolin G20 karo na 19, ya bayyana cewa, akwai bukatar kungiyar G20 ta ci gaba da yin aiki a matsayin wani ginshiki na inganta gudanar da harkokin duniya, da ciyar da tarihi gaba, da samar da babban ra'ayi da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai a fannonin tattalin arziki, kudi, cinikayya, fasahar zamani da inganta muhalli, da dai sauransu, a cewar kakakin.

Don haka, ya kamata kungiyar G20 ta karfafa hadin gwiwar tattalin arzikin duniya, da samar da yanayi mai bude kofa, da hada kai, da rashin nuna bambanci ga hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen duniya, da kara yawan fada-a-ji da wakilcin kasashe masu tasowa, da kiyaye tafiyar da kasuwannin hada-hadar kudi na duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)