logo

HAUSA

Xi ya mika sakon taya murna ga babban taron intanet na duniya na bana a Wuzhen

2024-11-20 12:07:05 CMG Hausa

A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga babban taron intanet na duniya na bana da ake yi a garin Wuzhen ta hanyar bidiyo.

Xi ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, sabon zagaye na juyin-juya-halin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen masana'antu na samun bunkasa cikin sauri, kuma ana samun sabbin fasahohi irin su fasahar kirkirarriyar basira, wadanda suka kara inganta karfin fahimtar dan Adam da sauya fasalin duniya, ko da yake lamarin ya kuma zo da kasada da sauran kalubalen da ba a zata ba.

Shugaba Xi ya ce ya kamata a fahimci yanayin fasahar zamani gaba daya, da hanyoyin sadarwa da ci gaban fasaha, da daukar sabbin kirkire-kirkire a matsayin karfin gudanarwa na farko, sannan tsaro a matsayin ginshiki, da ci gaba mai hadaka a zaman neman mutuntawa, kana a habaka bullo da sabbin abubuwa cikin hanzari, da samar da aminci a harkokin intanet da kuma yin aiki tare don samar da kyakkyawar makoma ta fasahar zamani.

Shugaban ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashe, wajen daukar mataki da zai kafa tarihi a bangaren juyin-juya-halin fasahar sadarwa, da gina al'umma mai makoma mai kyau a bangaren harkokin intanet da kuma sanya intanet din ya zama mai amfani ga jama'a da duniya baki daya.

An bude babban taro na duniya a kan intanet na shekarar 2024 na Wuzhen, a wannan ranar ce a garin Wuzhen dake birnin Tongxiang na lardin Zhejiang, mai taken "Rungumar kyakkyawar makomar dan Adam ta fasahar zamani mai kaifin basira-aiki tare don gina al'umma mai makoma mai kyau a bangaren harkokin intanet. (Abdulrazaq Yahuza Jere)