Nijar na karbar bakuncin taron kasa da kasa domin hadin kai da yaki da mulkin mallaka
2024-11-20 09:31:50 CGTN Hausa
A jamhuriyyar Nijar, wani taron kasa da kasa da aka kebe kan yaki da mulkin mallaka da hadin kai tare da al'umomin yankin Sahel ya bude a ranar jiya Talata 19 ga watan Nuwamban shekarar 2024 a zauren taruka na kasa da kasa na Mahamat Gandhi dake birnin Yamai a karkashin jagorancin faraminista Ali Mahamane Laminie Zeine.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.