Gwamnatin Najeriya ta ce ta himmatu sosai wajen sake fasalta tsarin shari'ar kasar
2024-11-20 09:21:36 CMG Hausa
Ministan shari'a na tarayyar Najeriya Mr. Lateef Fagbemi ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a da su hada karfi wajen shawo kan dukkan kalubalen da ayyukan shari'a a kasar ke fuskanta.
Ya bukaci hakan ne jiya Talata 19 ga wata a garin Ilorin ta jihar Kwara ta Najeriya lokacin da yake gabatar da jawabi a babban taron kasa kan batun garambawul a bangaren shari'a.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.