Gwamnatin jihar Kebbi ta kulla alaka da kasar Indonesia a fagen sha’anin kiwon dabbobi a zamanance
2024-11-19 08:15:46 CMG Hausa
Gwamnatin jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya ta kulla alaka da kasar Indonisiya a fagen sha’anin bayen shanu da sabbin dabarun kimiya na zamani da za su samar da jinsin dabbobi masu saurin yaduwa da wadatar nama da kuma madara.
Kwamishinan harkokin addini na jihar Alhaji Sani Aliyu ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 16 ga wata a birnin Kebbi lokacin da yake ganawa da manema labarai biyo bayan ziyarar da gwamnan jihar Alhaji Nasir Idris ya kai kasar ta Indonesia a kwanakin baya.
Daga tarayyar Najeriya wkailinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kwamishinan ya ce, a karkashin wannan alaka da aka kulla, a kwanan nan gwamnatin kasar Indonesiya ta dauki nauyin wasu likitocin dabbobi guda biyu daga Kebbi domin dai samun horon kwanaki 30 a kasar inda za a mayar da hankali wajen horas da su hanyoyin zamani na yin baye da zummar idan sun dawo gida za su yi amfani da kwarewar da suka samu wajen bunkasa sha’anin kiwon dabbobi a jihar, ha’ila yau kuma an tsara cewa wasu kwararrun likitocin dabbobi daga kasar ta Indonesiya za su zo jihar ta Kebbi bayar da horo ga likitoci masu yawa, inda ya ce, sanin kowa ne cewa jihar ta Kebbi ita ce a kan gaba a jihohin dake arewacin Najeriya da take da makiyaya da dama.
Alhaji Sani Aliyu ya tabbatar da cewa zuwa karshen wannan wata da muke ciki, jakadan kasar ta Indonesiya a Najeriya zai kawo ziyara jihar ta Kebbi domin sake karfafa wannan alaka. (Garba Abdullahi Bagwai)