logo

HAUSA

Shugabanin kasashen Sin da Argentina sun gana a gefen taron kolin G20

2024-11-19 23:57:49 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Talata ya gana da shugaban kasar Argentina Javier Milei a gefen taron kolin kungiyar G20 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. 

Kasashen Sin da Argentina sun yi alkawarin ba da goyon baya wajen inganta raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” a ganawar. 

Da yake karin haske game da makomar hadin gwiwar da za a yi gaba, Xi ya ce, tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasashen Sin da Argentina sun yi matukar dacewa da juna, yana mai bayyana fatan bangarorin biyu za su iya fadada hadin gwiwa a fannonin makamashi, da samar da ababen more rayuwa na ma'adinai, da aikin gona, da kimiyya da fasaha, da tattalin arziki na dijital. (Yahaya)