logo

HAUSA

An kaddamar da bikin kafofin watsa labaru kan raya harkokin matasan kasashe masu tasowa a birnin Rio de Janeiro

2024-11-19 10:46:53 CMG Hausa

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake halartar taron koli na 19 na kungiyar G20 a birnin Rio de Janeiro tare da ziyara a kasar Brazil, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, da hadin gwiwar taron kolin matasa na kungiyar G20 wato Y20, da sakatariyar fadar shugaban kasar Brazil, sun kaddamar da bikin kafofin watsa labaru kan raya harkokin matasan kasashe masu tasowa a jiya Litinin, inda kafofin watsa labaru 215 daga kasashe 74 suka gabatar da kiran kasashe masu tasowa kan sa kaimi ga raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma.

A jawabinsa, shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, CMG tare da kafofin watsa labaru abokan hulda, sun kaddamar da wannan biki tare, don kafa wani dandalin yin mu’amala, da kuma sa kaimi ga matasan kasashe masu tasowa su yi hadin gwiwa da samun ci gaba a fannonin watsa labarai, da gwada fasahohi, da binciken al’ummu, da mu’amala a fannin wasannin motsa jiki, da sauransu. (Zainab Zhang)