Shugaba Xi Jinping ya ce kasar Sin da Birtaniya na da dimbin sararin yin hadin gwiwa
2024-11-19 00:14:22 CMG Hausa
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa kasarsa da kasar Birtaniya suna da dimbin sararin yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Ya fadi hakan ne a yayin da yake tattaunawa da firaministan Birtaniya Keir Starmer, a gefen taron kolin shugabanni na kungiyar G20 a ranar Litinin a birnin Rio de Janeiro.
Yayin da yake bayyana cewa a halin yanzu duniya ta shiga wani sabon yanayi na yamutsi da samun sauyi, Xi ya ce a matsayinsu na kasashen da suke da kujerun dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kuma manyan masu karfin tattalin arziki a duniya, duka kasashen biyu suna da alhakin bunkasa ci gabansu na cikin gida da kuma magance kalubale mai yawa dake addabar duniya.
Shugaba Xi ya ce ko da yake akwai bambancin tarihi, al’adu, dabi’u da tsarin zamantakewa a tsakanin kasashensu, amma kuma kasashen biyu suna da muradu masu yawa da suka yi tarayya da juna.
Ya kara da cewa, ya kamata kasar Sin da Birtaniya su yi na’am da mataki da fahimtar ci gaban juna, da kyautata hulda da zurfafa amincewa da juna ta fannin siyasa domin tabbatar da cewa dangantakar kasar Sin da Birtaniya ta dore babu tangarda zuwa tsawon lokaci. (Abdulrazaq Yahuza Jere)